ABNA24 : Jaridar Egypt Daily ta bayyana cewa tuni tsarin yanar gizo mafi karfi a duniya wato G5 ya fara sauya rayuwar masu amfani da shi a kasashen duniya da dama, daga cikin tsarin ya sa suka rage amfani da tsarin samar da yanar gizo wanda ake kira WiFi a gidajensu, don irin karfi da kuma saurin biyan bukatu wanda tsarin na G5 yake bayarwa.
Kamfanin Ericsson ConsumerLab ya ce, ya gudanar da bincike a wasu kasuwannin kamfanin 26 a kasashe daban-daban, wadanda kuma suka hada da Amurka, Cana, Kurea ta Kudu, da kuma Burtania, inda ya gano cewa duk 1 daga cikin mutane 5 masu amfani da G5 sun rage amfani da Wifi a gidajensu.
Labarin ya kara da cewa, ya zuwa yanzu a cikin mutane kimani biliyon 1.3 masu amfani da wayar salula a duniya, miliyon 220 daga cikinsu suna amfani da tsarin yanar gizo na G5 ne. Daga karshe rahoton ya kammala da cewa tsarin bada internet na G5 ya samu Karin karbuwa ne a lokutan kulle wadanda ake ta yi a kasashen duniya saboda hana yaduwar cutar korona.
342/